Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-17 10:45:37    
Sabunta: An rufe taron duniya kan batun Darfur a Libya

cri
Ran 16 ga wata, a birnin Tripoli, hedkwatar kasar Libya, an rufe taron duniya kan batun yankin Darfur na kasar Sudan. Sanarwar karshe da aka zartas da ita a gun taron ta tabbatar da muhimmiyar rawar da Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen da ke makwabtaka da kasar Sudan suke takawa wajen daidaita batun Darfur ta hanyar siyasa. Bangarori daban daban da abin ya shafa sun nuna babban yabo kan sakamakon taron.

Waklin musamman na kasar Sin Liu Guijin mai kula da batun Darfur ya halarci taron, inda ya yi bayani kan ra'ayi da matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai kan daidaita batun Darfur. Ya bayyana cewa, don sa kaimi kan daidaita wannan batu ta hanyar siyasa, ya kamata kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Sudan su taka muhimmiyar rawa.

A wannan rana, a gun taron manema labaru da aka yi a birnin New York, babban sakatare Ban Ki-Moon na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa, girke sojojin hadin gwiwa na kiyaye zaman lafiya mataki ne na farko wajen shimfida zaman lafiya a Darfur, daga bisani kuma, ya kamata a karfafa gwiwar bangarorin da abin ya shafa da su daddale yarjejeniyar siyasa na din din din, ta haka za a tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankin.

A cikin jawabinsa na rufe taron, manzon musamman na kungiyar AU Salim Ahmed Salim ya jaddada cewa, taron da aka yi a wannan karo ya ba da muhimmin tasiri kan Darfur da duk kasar Sudan. Taron ya kuma shaida cewa, lokaci ya yi da za a maido da shawarwarin zaman lafiya da aiwatar da shirin taswirar ayyukan siyasa.(Tasallah)