Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-16 10:01:34    
An soma taron duniya kan batun Darfur a kasar Libya

cri

A ran 15 ga wata a birnin Tripoli na kasar Libya, an soma taron kasa da kasa kan batun Darfur na kasar Sudan. A gun taron, za a yi kokarin daidaita ra'ayoyin bangarori daban-daban da matsayinsu domin share fagen farfardo da shawarwarin shimfida zaman lafiya da ayyukan siyasa a shiyyar Darfur.

A gun bikin kaddamar da taron, Mr. Jan Eliansson, manzon musamman na M.D.D. ya yi kira ga bangarori daban-daban da suke da nasaba da batun Darfur da su kara yin hadin guiwa domin bude sabon shafi domin farfardo da shawarwarin. Ya ce, lokaci ne na farfado da yin shawarwari, bangarori daban-daban za su yi shawarwari kai tsaye a tsakaninsu a mataki mai zuwa. A waje daya, Mr. Eliasson ya nemi bangarori daban-daban da su dauki nauyin da ke bisa wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a shiyyar Darfur.

A cikin jawabin da ya bayar, malam. Salim Ahmed Salim, manzon musamman na kungiyar Tarayyar Afirka ya yaba wa kokarin da bangarori daban-daban suka bayar domin farfado da yin shawarwari. Ya kuma yi kira ga kunigiyoyi masu adawa da gwamnatin Sudan da su yi shawarwari da gwamnati tun da wuri domin daidaita batun Darfur.

A cikin nasa jawabin, Mr. Al Sammani Al Wasila, shugaban tawagar wakilan Sudan kuma karamin ministan harkokin waje na kasar Sudan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sudan tana cike da imanin cewa, ba za a iya daidaita batun Darfur ta hanyar soja ba, sai dai an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kawai a shiyyar ta hanyar zaman lafiya, wato shigar da bangarori daban-dabam a cikin wannan ayyukan shimfida zaman lafiya a shiyyar.

Malam Ali al-Traiki, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Libya wanda ke kula da harkokin Afirka ya kuma yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sudan ta bayar domin daidaita batun Darfur ta hanyar zaman lafiya. (Sanusi Chen)