Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-10 19:06:56    
Tsohon gari na Luzhi na lardin Jiangsu

cri

Wata sigar musamman daban ta Luzhi ita ce tsofaffin itace. Yanzu ana kare tsofaffin itacen Gingko guda 7 a garin, a ciki kuma tsawon shekaru na mafi tsoho ya kai misalin dubu 1 da dari 5. Madam Wang Yan ta yi wa masu yawon shakatawa bayani cewa, akwai tsofaffin itace da suke fi ban mamaki 3 a Luzhi, ta ce, 'Da farko akwai wani icen Wolfberry mai tsawon shekaru fiye da 120. Na biyu shi ne icen furen Wisteria sinensis mai tsawon shekaru fiye da dari da ke girma a kusa da wani ice mai tsawon shekaru dari, furanninsa na da kyan gani sosai, sun kuma bayar da kamshi. Na uku kuma shi ne icen Gingko mai tsawon shekaru 1500.'

Madam Wang ta kara da cewa, masu yawon shakatawa suna iya kallon wadannan itace 3 a gidan ibada na Baoshengsi da ke titin yamma a Luzhi. An gina wannan gidan ibaba a shekarar 503, wato ke nan tsawon shekarunsa ya kai 1500 ko fiye. Gidan ibadan da ake gani a yau gidan ibada ne bayan da aka yi masa kwaskwarima. Har zuwa yanzu ana ajiye abubuwan sassaka na zamanin daular Tang wato tsakanin shekarar 618 zuwa ta 907 da gine-gine na zamanin daular Ming wato tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1644 na kasar Sin da sauran kayayyakin gargajiya. Duk da haka, mutum-mutmin Arhats da aka sassaka su a jikin bango sun fi daraja a gidan ibada na Baoshengsi.

An sassaka wadannan mutum-mutumin Arhats yau da shekaru fiye da 1000 da suka wuce, sun sha bamban da saura saboda an sassaka su a jikin bango, a maimakon an saka su daya bayan daya a kan kasa.

A tsohon garin Luzhi, masu yawon shakatawa ba kawai sun iya ziyarar gidan ibada da kuma yin yawon a kan gadoji na gargajiya, da kallon kayayyakin gargajiya da tsofaffin itace ba, har ma sun iya gano wani sabon wuri mai ni'ima ba da gangan ba a lokacin da suke yawo a kan titunan Luzhi.


1 2