Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-10 17:44:16    
Mutanen da su kan ji gajiya sosai wajen aiki sun fi saukin samun kiba fiye da kima

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, mutanen da su kan ji gajiya sosai wajen aiki sun fi saukin samun kiba fiye da kima, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin tana kara sa ido kan ayyukan kiwon lafiya domin kiyaye hakkin fararen hula. To, yanzu ga bayanin.

Manazarta na kasar Birtaniya sun gano cewa, mutanen da su kan ji gajiya sosai wajen aiki sun fi saukin samun kiba fiye da kima, shi ya sa ya kamata mutane masu shan aiki sosai su sassauta gajiya da suke ji da kansu.

Ta yin nazari a fannin ilmin likitanci, an riga an gano cewa, irin wannan gajiya da a kan ji wajen aiki a dogon lokaci yana da nasaba da cututtukan zuciya da na sauye-sauyen halittu. Amma a cikin wannan nazarin da Eric Brenner da abokan aikinsa na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar London ta kasar Birtaniya suka yi, sun gano cewa, idan gajiya da masu aikin yi suka ji ta karu, sai yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su za ta karu.

Manazarta sun gudanar da wani bincike na tsawon shekaru 19 ga maza 6895 da kuma mata 3413 wadanda shekarunsu ya kai 35 zuwa 55 da haihuwa. A cikin binciken, wadannan mutane sun gabatar da takardun tambayoyi game da gajiyar da su kan ji wajen aiki na lokaci-lokaci. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da wadanda suka amince da jin gajiya sosai wajen aiki a cikin takardun tambayoyi har a kalla sau uku, yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su ta karu da kashi 73 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su taba jin gajiyar aiki ba.

Sabo da haka Mr. Brenner yana ganin cewa, wannan sakamakon bincike ya samar da wata muhimmiyar shaida kan cewa, gajiya wajen aiki ita ce muhimmin dalilin da ke haddasa samun kiba fiye da kima.

Jin gajiya sosai ba kawai zai haddasa mutane su samu kiba fiye da kima ba, har ma game da wadanda suke fama da sankara, zai yi illa ga warkar da su.

Ta yin nazari, masu ilmin kimiyya na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Wake Forest ta kasar Amurka sun gano cewa, lokacin da ake jin gajiya ko damuwa, wani sinadarin hormone da ke cikin jikin dan Adam wanda ake kiransa adrenaline zai haddasa sauye-sauyen kwayoyin sankarar mama da mafitsara, ta haka kwayoyin sankara za su iya yin dagiya da dabarun jiyya na kashe su.

Manazarta sun ba da wani rahoto cewa, sun yi nazari kan kwayoyin sankarar mama da na sankarar mafitsara a cikin dakin gwaje-gwaje, daga baya kuma sun gano cewa, lokacin da kwayoyin sankara suke tare da sinadarin adrenaline, wani sinadarin da ke iya kashe kwayoyi ba zai iya yin aiki kamar yadda ya kamata ba, shi ya sa ba a iya kashe wadannan kwayoyin sankara ba.

Sabo da haka George Kulik wanda ya kula da wannan nazari ya bayyana cewa, game da masu fama da sankara wadanda suka fi saukin jin damuwar tunani, kamata ya yi su sassauta gajiya da su kan ji domin ba da taimako ga dabarun jiyya.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin tana kara sa ido kan ayyukan kiwon lafiya domin kiyaye hakkin fararen hula.