Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-06 16:01:54    
Kasar Sin ta gano wani babban filin man fetur da yawansa ya wuce ton biliyan 1

cri

Daga baya dai, wannan kamfanin kasar Sin ya gano gurbataccen man fetur mai yawa da ke shimfidu a karkashin wurin Nanpu ta hanyar sabuwar fasaha. Malam Zhou Haimin, babban manajan filin men fetur na Jidong na kamfanin ya bayyana cewa, "ko da yaushe, muna nacewa ga ra'ayinmu cewa, tabbas ne, ya kasance da wani babban filin man fetur a wurin Nanpu da muke bincike. Bayan da muka shafe shekaru hudu muna ta binciken, daga bisani, mun gano wani babban filin man feter wanda nauyansa ya wuce tan biliyan 1."

Malam Jia Chengzao, mamban cibiyar kimiyya ta kasar Sin kuma mataimakin shugaban kamfanin hannun jari na man fetur na kasar Sin ya bayyana cewa, wannan sabon filin man fetur da aka gano yana da muhimmanci sosai ga ba da tabbaci don samar da man fetur da gas yadda ya kamata a kasar Sin. A sakamakon bincike da ake zurfafa, za a kara gano gurbataccen man fetur da ke shimfidu a karkashin wurin. Ya kara da cewa, "an gano irin wannan babban filin man fetur wanda ke dab da yankin tattalin arziki na hedkwatar kasa, kuma a yankunan raya tattalin arziki na gabashin kasar Sin. Lalle, wannan yana da muhimmanci sosai ga kasar Sin don ba da tabbaci ga samar da man fetur da gaz yadda ya kamata. Nan gaba, kamata ya yi, a kara kokari wajen yin bincike ta hanyar sabuwar fasaha, kuma mai yiwuwa ne, za a kara gano babban filin man fetur da gas a wurin."


1 2 3