Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-30 14:20:08    
Yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai fiye da miliyan 2 cikin shekara 1 da ta gabata

cri
A ran 29 ga wata, ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin ta bayar da labari, cewar tun daga ran 1 ga watan Yuli na shekarar bara zuwa karshen watan Yuni na shekarar da muke ciki, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya kai miliyan 2 da dubu 20. A waje daya, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu ta wannan hanyar dogo ya kai ton kimanin miliyan 11.

Wani babban jami'in ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin ya bayyana cewa, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet yau da shekara 1 da ta shige, hanyar dogo da injuna da na'urori da ma'aikata da fasahohin yin amfani da wannan hanyar dogo sun ci jarrabawar da sauye-sauyen yanayin duniya suka yi musu a cikin lokuta daban-daban. Ba a haddasa hadarurukan zirga-zirga, babu aukuwar hadarin mutuwar ma'aikata ko fasinjoji a kan wannan hanyar dogo a cikin wannan shekara 1 da ta shige.

Bugu da kari kuma, an tsara manufofi masu tsanani iri iri bisa "Dokar Kiyaye Muhalli" da "Dokar Kiyaye Namun Daji" na kasar Sin domin kiyaye muhalli a kan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet. (Sanusi Chen)