Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-29 21:35:45    
Ana kiyaye hanyar namun daji da ke ratsa hanyar dogo ta Qinghai Tibet

cri

A kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga ma'aikatar hanyar dogo ta kasar Sin cewa, kamfanin hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya gyara hanyoyi 33 domin namun daji wadanda suke ratsa hanyar dogo ta Qinghai-Tibet domin kiyaye wadannan namun daji da suke zama a wurn. A waje daya an kafa shingogi da alamomi da na'urorin da ke nuna wa namun daji hanyar da ya kamata su bi domin kiyaye su.

Lokacin da ake shimfida hanyar dogo ta Qinghai-Tibet yau da wasu shekaru da suka wuce, kwararru sun yi nazari kan zaman rayuwar namun daji da suke zama a wuraren da ke dab da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet domin neman hanyar kiyaye su.

Kwanan baya, babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta yi bincike da dudduba ayyukan kiyaye muhalli da aka yi a kan hanyar dogo ta Qing-Tibet. Sakamakon binciken da aka yi ya bayyana cewa, hanyoyi 33 da aka shimfida da tsawonsu ya kai kusan kilomita 60 domin kiyaye namun daji suna da amfani sosai. (Sanusi Chen)