Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-23 20:01:20    
Taron kara wa juna sani kan muhimmiyar doka a Hongkong

cri
An gudanar da wani taron kara wa juna sani kan muhimmiyar doka jiya Jumma'a a yankin Hongkong a albarkacin ranar cika shekaru 10 da aka maido da Hongkong a karkashin mulkin kasar Sin. Kwararru fiye da 100 da suka yi suna a fannin doka, wadanda suka fito daga babban yankin kasar Sin, da Hongkong, da Macau, da kuma shiyyoyin ketare sun waiwayi halin da aka aiwatar da babbar doka a yau da shekaru 10 da suka wuce a Hongkong, kuma sun yi hangen nesa a kan kalubalen da Hongkong zai fuskanta a nan gaba.

Madam Liang Aishi, mataimakiyar daraktar kwamitin babbar doka ta mazaunan Hongkong ta kwamitin din din din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ta bayyana a lokacin da take yin jawabi a gun taron kara wa juna sani cewa, marigayi Deng Xiaoping ya gabatar da babban tsarin "kasa daya, amma tsarin mulki guda biyu", domin maido da Hongkong a karkashin mulkin Sin, wannan dai ya bayyana hikimar siyasa da halin yin hakuri na jama'ar Sin. Shirya da tsara babbar dokar, ya zayyana irin kyakkyawan zane na maido da Hongkong a karkashin mulkin Sin kamar yadda ya kamata, amma ana bukatar al'ummar Hongkong da su kara fahimtar babbar dokar, domin aiwatar da ita lami lafiya.

Shugaban hukumar kula da harkokin siyasa ta gwamnatin mazaunan Hongkong Lin Ruilin, ya bayyana a gun taron kara wa juna sanin cewa, tun shekaru 10 da suka wuce da aka maido da Hongkong a karkashin mulkin Sin, gwamnatocin kasashen waje, da kafofin watsa labaru na duniya, da kuma jama'ar Hongkong, dukansu sun amince da cewa, ba kawai ana iya aiwatar da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu" ba, har ma tsarin na da amfani sosai. (Bilkisu)