Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 17:03:15    
Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta zuba jari kusa da kudin Sin yuan biliyan 78, domin raya Tibet tun daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2010

cri

Tun daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2010, gwamnatin tsakiyar kasar Sin za ta zuba jari kusa da kudin Sin yuan biliyan 78, domin gine-ginen manyan ayyuka na Tibet, da kyautata halin zaman rayuwar manoma da makiyaya.

Shugaba Qiangba Puncog na jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, ya fayyace haka ne a gun taron manema labaru da aka shirya a yau 20 ga wata a nan birnin Beijing.

Mr. Qiangba Puncog ya bayyana cewa, jihar Tibet ta samu saurin bunkasuwa a karkashin goyon baya sosai da gwamnatin tsakiyar Sin ta nuna mata. Ba kawai gwamnatin tsakiyar ta tsara manufofi da matakai na fifiko a jere da ke da amfani kan bunkasuwar Tibet ba, har ma ta zuba jari da yawa, domin goyon bayan bunkasuwar Tibet. Kamar misali, a cikin kudin Sin yuan 10 da jihar Tibet ta kashe, akwai yuan 9 da suka fito daga gwamnatin tsakiyar.

Bisa labarin da muka samu an ce, a shekarar da ta wuce, yawan kudin da aka samu daga wajen aikin kawo albarka a duk jihar Tibet ya kai kudin Sin yuan biliyan 29, wato yana ta karuwa da kashi sama da 12 cikin dari a jere a cikin shekaru 6 da suka wuce, yawan kudin da ko wane mutum ya samu daga wajen kawo albarka ya wuce kudin Sin yuan dubu 10. (Bilkisu)