Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-04 16:08:23    
Xu Yirong, wani kwararren kasar Sin wajen shinkafa

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wani kwararren kasar Sin a fannin ayyukan gona wanda ake kiransa Xu Yirong. Malam Xu ya samu manyan nasarori da yawa a fannin shuka shinkafa kamar yadda Yuan Longping ya yi, wani shahararren mai ilmin kimiyya na kasar Sin wajen nazari kan shinkafa mai aure.

Har kullum Xu Yirong yana dukufa kan yin nazari kan shuka shinkafa a shiyya mai sanyi da ke arewacin kasar Sin domin dubban manoma da ke arewacin kasar su iya kara samun shinkafa da nauyinta ya kai kilogram biliyan gomai a ko wace shekara. Sabo da haka ake kiransa "kwararre a fannin shuka shinkafa a wurare masu sanyi".

Duk da haka, har kullum Mr. Xu ya kan fadi cewa, ni ba kwararre ba ne, ni wani mai shuka shinkafa ne kawai.

"Bambancin da ke tsakanin manoma da ni shi ne na riga na shuka shinkafa cikin dogon lokaci, na fara gudanar da wannan aiki daga shekara ta 1951. Ban da wannan kuma ina da ilmin musamman wajen shuka shinkafa idan an kwatanta ni da manoma. Amma game da fasahohin shuka shinkafa, manoma sun fi kyau."

Ko da yake Xu Yirong wanda shekarunsa ya kai kusan 83 da haihuwa yana da furfura, amma idanunsa sun yi kyalkyali. Yana mai da hankalinsa a kan nazarin shinkafa a duk rayuwarsa. Mutanen da suka fahimce shi sosai sun san cewa, wurin da yake so shi ne gonaki, kuma batun da ya fi son tattaunawa a kai shi ne shinkafa. Ya kan tattauna da manoma kan shinkafa a gonaki, kuma bai taba mayar da kansa a matsayin wani kwararre ba.

Kaunar da Malam Xu ya nuna ga nazarin shinkafa tana da nasaba da zaman rayuwarsa sosai. A shekara ta 1924, an haife shi a birnin Beining na lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Lokacin da yake makaranta, sojojin kasar Japan sun fara kawo wa kasar Sin hare-hare, sabo da haka fararen hula na kasar Sin sun sha wahaloli sosai. Kuma Malam Xu ya gaya mana cewa,

"a idon mahara Japanawa, Sinawa ba su iya cin shinkafa ba, ba su cancanci cin shinkafa ba. Shi ya sa a bikin bazara wato ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a kan ci shinkafa kadan a boye."

Tun wancan lokaci, Malam Xu yana da wani buri, wato a wata rana, dukkan Sinawa za su iya cin shinkafa. Sabo da yankunan da ke arewa maso gabashin kasar Sin suna da sanyi sosai, shi ya sa ba a iya samar da shinkafa da yawa ba. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekara ta 1949 ba da jimawa ba, Xu Yirong da ya gama karatunsa daga jami'a ya je wani filin gonaki na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin domin yin nazari kan shuka shinkafa a wurare masu sanyi.

Amma sabo da wasu dalilan tarihi, an tilasta wa Xu Yirong da ya yi watsi da wannan nazari. Bayan shekaru goma, ya sake dawo da cibiyar nazarin shinkafa ta lardin Hei Longjiang. A wancan lokaci, shekarunsa ya riga ya kai 60 da haihuwa, ya kamata ya yi ritaya. Amma a idon Malam Xu, an hada shinkafa da ransa tare, kafin ya samu ci gaba a fannin shuka shinkafa a wurare masu sanyi, ba zai bar shinkafa ba. Kuma ya bayyana cewa,

"har kullum ina yin nazari kan shinkafa, shi ya sa nake nuna kauna sosai gare shi, duk ranar da ban gan shi ba, na kan ji bakin ciki."

Bayan da ya yi gwaji har shekaru fiye da goma, Malam Xu ya cimma nasara wajen samun fasahar shuka shinkafa a wurare masu sanyi. Sai nan da nan ya gabatar da wannan fasaha ga manoman da ke wurare masu sanyi, da kuma yada fasahar a filayen gonaki. A karkashin jagorancin Malam Xu, manoma sun samu amfanin gona mai armashi, kuma sannu a hankali sun samu wadata, shi ya sa manoma suke nuna wa Xu Yirong girmama kwarai da gaske.

Bugu da kari kuma, domin tabbatar da samar da shinkafa mai dimbin yawa kamar yadda ya kamata, ta yin nazari, Malam Xu ya samu wata dabarar musamman wajen tabbatar da cututtukan da shinkafa ta kan kamu da su. Qu Zonggui, wani manomi wajen shuka shinkafa ya nuna yabo sosai ga irin wannan dabara. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"Malam Xu ya zo gonakina, da kuma cire wata karar shinkafa, daga baya kuma ya zaro wata wuka daga aljihunsa. Ganin haka, muna jin mamaki sosai. Kowa ya sani likitoci su kan yi wa wadanda suke fama da cututtuka tiyata, amma ba mu taba ganin yi wa shinkafa tiyata ba a da."

Har zuwa yanzu Malam Xu yana gudanar da aikinsa a gonaki domin ci gaba da yin nazari kan shinkafa, ta yadda manoman shuka shinkafa na kasar Sin za su iya samun wadata.(Kande Gao)