Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-31 18:42:47    
Sanya wa Sudan sabon takunkumi ba zai ba da taimako wajen warware batun Darfur ba

cri

A ran 31 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta yi bayani a birnin Beijing, cewa a cikin wannan halin da ake ciki yanzu, sanya wa kasar Sudan sabon takunkumi ba zai ba da taimako wajen warware batun Darfur ba, sai dai zai tsananta halin da ke ciki.

Haka kuma Madam Jiang ta ce, a 'yan shekarun nan da suka gabata, batun Darfur ya samu ci gaba bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi tare, kuma gwamnatin kasar Sudan da MDD da kungiyar AU sun samu ra'ayi daya kan shiri na mataki na biyu da tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan ya gabatar. Yanzu gwamnatin Sudan tana jiran MDD da kungiyar AU da su gabatar da shiri kan aiwatar da shiri na mataki na uku.

Madam Jiang ta kuma yi kira ga bangarori daban daban da su yi hakuri da ci gaba da tattaunawa da shawarwari tsakaninsu wajen aiwatar da shirin kiyaye zaman lafiya na mataki na uku da Kofi Annan ya gabatar daga dukkan fannoni domin sai kaimi ga yunkurin shimfida siyasa a shiyyar Darfur, da ci gaba da kyautata halin jin kai da tsaron kai da shiyyar ke ciki, ta yadda za a iya neman warware batun Darfur ta hanyar siyasa.(Kande Gao)