Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-24 15:48:01    
Wakilin musamman mai kula da batun Darfur na kasar Sin ya yi shawarwari da jami'an kasar Sudan

cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, a ran 23 ga wata, Liu Guijin wakilin musamman mai kula da batun Darfur na gwamnatin Sin ya yi musayar ra'ayinsa da jami'an kasar Sudan kan huldar dake tsakanin Sin da Sudan da batun Darfur da sauran batutuwa.

Mr.Liu Guijin ya bayyana cewa, huldar hadin gwiwa mai sada zumanci da aka kulla bisa tushen samun moriyar juna da daidai wa daida a tsakanin Sin da Sudan ta kara bunkasuwa cikin shekarun da suka wuce. Bangaren Sin ya yi yabo kan kokarin da gwamnatin Sudan da bangarorin da abin ya shafa suka yi duk domin sa kaimi ga warware batun Darfur, yana fatan bangaren Sudan zai nemi dabara da dama don aiwatar da shirin da Mr. Kofi Annan ya gabatar. Kan batun warware Darfur bangaren Sin yana son ba da amfani nasa mai yakini, kuma zai ci gaba da nuna jin kai da ba da taimako mai amfani don bunkasa shiyyar nan.

Bangaren Sudan ya yaba sosai kan dangatakar hadin kai mai sada zumanci a tsakanin Sin da Sudan, ya yi godiya ga bangraren Sin domin taimakomai amfani da gudummawar da ya bayar kan batun Darfur.

Ran nan a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan kuma, an mika wa gwamnatin Sudan sababbin kayayyakin da gwamnatin kasar Sin ta baiwa shiyyar Darfur ta Sudan.

A gun bikin sa hannu da mika wa juna yarjejeniya Mr. Liu Guijin ya ce, gwamnatin Sin tana lura da halin jin kai da ake ciki a shiyyar Darfur, tana nuna juyayi ga halin da mutanen Darfur ke ciki. Ya kara da cewa, ba ma kawai gwamnatin Sin ta samar da taimakonta na jin kai ba, hattama ta kara hadin kai da kasar Sudan a duk fannoni da taimaka wa Sudan ga bunkasa tattalin arzikinta da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na zaman al'umma don warware batun Darfur tun da wuri.(salamatu)