Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:37:00    
Shanghai tana share fagen taron wasannin Olympic na musamman na duniya yadda ya kamata

cri

A gun taron manema labaru da aka yi a nan Beijing a ran 17 ga wata, mataimakin zaunannen shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na musamman na Shanghai kuma matamakin magajin birnin Shanghai Zhou Taitong ya yi karin bayanin cewa, yanzu ana share fagen taron wasannin Olympic na musamman yadda ya kamata. Ya ce,

'Yanzu ana horar da alkalan wasa da ma'aikatan tsara ajandar gasanni, kuma ana saye da jarraba kayayyakin wasannin motsa jiki na musamman bisa shirin da aka tsara. Sa'an nan kuma, bisa ka'idar yin tsimin kudi a fannin shirya gasa, ana yin mashashan aikin wajen yin kwaskwarima kadan kan filayen wasa 34 da ake bukata a wannan karo, musamman ma ana dora muhimmanci kan biyan bukatar taron wasannin Olympic na musamma, ana kyautata gine-gine marasa shinge. A galibi dai za a kammala yin kwaskwarima kan filayen wasa a karshen wata mai zuwa.'

Mr. Zhou ya kara da cewa, a lokacin taron wasannin Olympic na musamman, kasar Sin za ta bai wa masu halartar taron hidimomi ta fuskar aikin sa kai da fassarawa da harhada labarai da zirga-zirga da samar da abinci da wurin kwana da tsaron lafiya da kiwon lafiya da dai sauransu. Yanzu an riga an fito da shirye-shiryen ayyuka da matakan da abin ya shafa don ba da tabbaci ga mataki daban daban, bayan wannan kuma, an soma dauka da kuma horar da masu aikin sa kai da likitocin musamman da kuma kwararru masu ilmin fassara, ana kuma shirya musu rawar daji.

A shekara ta 2002 ne birnin Shanghai ya ci nasarar samun damar shirya taron wasannin Olympic na musamman na duniya na shekara ta 2007 a madadin kasar Sin. Gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan taron wasannin motsa jiki na musamman, ta zartas da kafa kwamitin shirya taron wasannin Olympic na musamman da kuma kwamitin gudanarwa. Hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin da hadaddiyar kungiyar harkokin nakasassu ta kasar Sin da sauran hukumomin Sin sun gudanar da shirye-shirye cikin himma da kwazo. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayim minista Wen Jiabao da sauran muhimman jami'an Sin sun sha ba da umurni, inda suka bukaci lallai a sami nasarar shirya taron wasannin Olympinc na musamman.


1 2 3