Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 10:57:00    
Ya kamata a kirkiro sabbin tunanin hadin kai da tabbatar da samun moriya da nasara tare wajen kara hadin kai a tsakanin Sin da Afrika

cri

Yau 16 ga wata, firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin ya bayyana a birnin Shanghai na kasar Sin cewa, ya kamata a kirkiro sabbin tunanin hadin kai, da kara matsayin hadin kai, da kuma tabbatar da samun moriya da nasara tare a yayin da ake kara hadin kai a tsakanin Sin da Afrika.

A gun bikin bude taron shekara-shekara na majalisar bankin raya kasashen Afrika, wato ADB na shekarar 2007 da aka shirya a wannan rana, Mr. Wen Jiabao ya ce, a yayin da ake kara hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, ya kamata a hada kan ayyukan ba da taimako daga gwamnati da hadin kai a tsakanin kamfannoni, bugu da kari ya kamata a kara mai da hankali sosai kan ayyukan jin dadin jama'a, da hadin kan fasaha da horar da kwararru, kazalika kuma a sanya kasashe da jama'ar Afrika su samu moriya a hakika.

Bayan haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya yi kira ga kasashen duniya, musamman ma kasashe masu sukuni da su cika alkawarinsu game da taimaka wa Afrika, kuma su ba da taimako ga Afrika kan tabbatar da yunkurin neman dauwamammen ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma.

A matsayinsa na shugaban majalisar ADB, kuma shugaban bankin jama'ar kasar Sin, Zhou Xiaochuan ya ce, a gun taron shekara-shekarar, masu halartar taron za su tattauna batutuwa na yadda za a kara karfin goyon baya da ADB zai yi wajen ayyukan kawar da talauci a kasashen Afrika da kuma samun bunkasuwarsu, da kyautatta manufofin tattalin arziki na dukan fannoni na kasashen Afrika, da kuma kara karfin neman dauwamammen ci gaba.

Shugaban ADB Donald Kaberuka ya bayyana cewa, shirya taron shekara-shekarar ya ba da dama ga ayyukan kara dangantakar abokantaka ta hadin kai a tsakanin Afrika da Asiya.(Bilkisu)