Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 10:55:41    
Wata jaridar Zimbabwei tana ganin cewa, kara hadin kan harkokin kudi a tsakanin Sin da Afrika yana da amfani kan kara yin ciniki da Afrika ke yi

cri

A gabannin ranar kiran taron shekara-shekara na majalisar bankin raya kasashen Afrika, wato ADB a birnin Shanghai na kasar Sin, jaridar The Herald, wato jaridar gwamnatin kasar Zimbabwei ta bayar da labari cewa, kara hada kai a tsakanin hukumomin harkokin kudi na Afrika da Sin yana da amfani kan kara yin ciniki a tsakanin Afrika da Sin, a waje daya kuma, yana da amfani kan kara yin ciniki da sauran shiyyoyi da Afrika ke yi.

Labarin ya ce, ADB ya shirya taron shekara-shekara na majalisa a kasar Sin, wannan yana da ma'anar tarihi sosai, zai bude sabon shafi ga hadin kai a tsakanin Sin da Afrika. Labarin ya jaddada cewa, ko da ya ke kasashen Afrika sun riga sun kafa hukumomin harkokin kudi daban daban na raya kasa, domin sa kaimi ga gine-ginen manyan ayyukan kasa da kuma bunkasuwar masana'antu, amma yawancinsu sun rasa fasahohi sabo da an kafa su ba da dadewa ba, don haka, suna bukatar kafa dangantakar abokantaka tare da hukumomin harkokin kudi na kasar Sin.

Labarin ya yi kira ga ADB da bankin shigi da fici na Afrika, da dai sauran hukumomin harkokin kudi da su sa kaimi ga hadin kai a tsakanin Sin da Afrika ta hanyar musayar ilmi da juna, da kuma sauran hanyoyi, ta yadda kasar Sin za ta kara fahimtar kasuwar Afrika. (Bilkisu)