Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 21:55:30    
Masu masana'antu na Sin da Afirka sun hadu a Shanghai don neman hadin gwiwa

cri

Yau Talata a nan birnin Shanghai, na yi hira da wani dan kasuwa mai masana'anta na kasar Sin, wato malam Li Mouxiang, wanda ya kasance shugaban darektocin wani kamfanin yin kayayyakin bunkasa wutar lantarki da ke nan kasar Sin, wanda kuma ya zo birnin Shanghai ne don halartar taron dandalin tattaunawa da aka yi a tsakanin masu masana'antu na kasashen Sin da Afirka.

Malam Li Mouxiang yana son zuwa kasar Sudan don zuba jari da bunkasa harkokin samar da wutar lantarki a kasar, kuma ya zo wajen taron ne don neman abokin hadin gwiwa, kuma ga shi taron ya samar da wani dandalin cudanya da juna a tsakanin masu masana'antu na Sin da Afirka.

Malam Li Mouxiang ya ce, ya amfana sosai daga wajen taron, musamman ta fuskar yadda za a rage hadarin zuba jari a Afirka da kuma neman abokin hadin gwiwa na bangaren Afirka.

A cikin 'yan shekarun nan, harkokin kasuwanci sun bunkasa sosai a tsakanin kasashen Sin da Afirka, musamman bayan taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a shekarar da ta gabata, irin wannan hadin gwiwa ya kara inganta. Game da irin wannan huldar hadin gwiwa, malam Li Mouxiang yana ganin cewa, huldar da ke karfafa a tsakanin gwamnatoci za ta iya sa kaimi ga bunkasuwar masana'antu. A sa'i daya, yana kuma ganin cewa, hadin gwiwar ya amfana wa bangarorin biyu gaba daya a maimakon bangare daya kawai ya ci moriya. A bayyane ne ya ce, 'a matsayina na wani dan kasuwa, dole ne ina neman cin riba domin kara bunkasa masana'anta, amma a hannu daya kuma, harkokin da zan tafiyar a Afirka za su kawo wa jama'ar wurin albarka, wanda kuma ya kasance babban nauyin da ke bisa wuyan masu masana'antun da suke son bunkasa harkokinsu a Afirka.

Bayan haka, na kuma sami damar yin hira da wani dan kasuwa mai masana'antar Carpet da ya zo daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, kuma ya zo kasar Sin kuma birnin Shanghai ne a karo na farko, domin taron shekara shekara da bankin ADB zai kira, kuma ya zo ne musamman don neman hadin gwiwa ta fuskar sha'anin kasuwanci, game da batun ko masana'antun Afirka sun amfana daga hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, ya ce, "babu shakka, akwai alheri cikin irin wannan hadin gwiwa, Sin ita ce babbar kasa a duniya, shi ya sa Afirka muke da sha'awa mu sami hadin gwiwa da sha'anin kasuwanci, akwai masana'antu iri iri da muke so mu yi koyi da su, kuma wannan hadin gwiwa ya ba mu damar san duk abubuwan da ake da su da kuma babbar kasuwar kasar Sin.(Lubabatu)