Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 21:40:28    
Yankin Lijiang na lardin Yunnan

cri

Asallamu alaikun, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan wani shahararren yanki da ke lardin Yunnan, sunansa Lijiang, daga baya kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Kallon tangaran masu launuka daban daban a birnin Jieshou na lardin Anhui'.

Yankin Lijiang yana da nisan kilomita misalin 590 a tsakaninsa da birnin Kunming, babban birnin lardin Yunnan, sa'an nan kuma, nisan da ke tsakaninsa da birnin Dali ya kai misalin kilomita 196 daga arewa.

Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi tsohon birni mai suna Lijiang a cikin takardar jerin wuraren tarihi na duniya a shekarar 1997 da ta gabata. Wannan birni yana nan ne a gindin tsaunukan da kankara mai taushi ke rufewa, shi ne dakin ajiye kayayyakin gargajiya wanda aka mayar da shi a matsayin garin 'yan kabilar Naxi, wadanda suka yi karni da dama suna bin al'adunsu na gargajiya. Ya zuwa yanzu dai 'yan kabilar Naxi suna zama a cikin gidajen gargajiya, suna samar da kide-kiden gargajiya, suna kuma yin bukukuwan gargajiya na al'adunsu cikin kuzari. Lijiang ta riga ta zama wata alama ce ga hukumar Yunnan a fannin yada aikin yawon shakatawa.

Yankin Lijiang ya sami saurin bunkasuwar aikin yawon shakatawa a cikin shekaru da dama da suka wuce saboda masu yawon shakatawa masu dimbin yawa sun kai ziyara a nan. Mutane su kan yaba wa kyan ganin Lijiang saboda shi wani tsohon birni ne, kuma shi gari ne ga daya daga cikin kananan kabilu 55 na kasar Sin. Saboda Lijiang na cikin karkara, shi ya sa 'yan kabilar Naxi suka ci nasarar kare kansu daga saurin bunkasuwar kasar Sin, suna ci gaba da zamansu na gargajiya.

A galibi dai, tsohon birnin Lijiang ne yake ta jawo masu yawon shakatawa da yawa. 'Yan kabilar Naxi suna zaune a wannan birni, wanda ake kiransa Dayan yau da shekaru misalin 800 da suka wuce. Ya zuwa yanzu dai iyalai fiye da 4000 suna zama a nan. Dukkan gidajen suna kasancewa kamar yadda aka gina yau da karni da dama da suka wuce.

Ban da gine-gine kuma, kide-kide su ne muhimman abubuwan tarihi na al'adu ga 'yan kabilar Naxi, wadanda aka shigar da su a yankin Lijiang a zamanin daular Ming wato a tsakanin shekara ta 1368 zuwa ta 1644. Sun bace a tsakiyar kasar Sin saboda yake-yaken da aka yi a cikin dogon lokaci. Tun daga zamanin daular Qing wato tun daga misalin shekara ta 1644, irin wadannan kide-kide na ci gaba da kasancewa a Lijiang mai kwanciyar hankali, wadda karkara ce.

To, masu sauraro, bayan da kuka dan huta kadan, bari mu ci gaba da shirinmu na yau.