Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 21:29:31    
Fiyarin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taimaka wa kasashen Afrika

cri

Yau 15 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a birnin Shanghai cewa, kasar Sin za ta yi iyakacin kokari don ci gaba da taimaka wa kasashen Afrika ta bankin raya kasashen Afrika, wato ADB da kuma sauran hanyoyi.

A lokacin da Mr. Wen Jiabao ya ke ganawa da Mr. Donald Kaberuka, shugaban ADB a wannan rana ya ce, tun bayan da aka shigar da kasar Sin cikin ADB a shekarar 1985, bangarorin biyu sun gudanar da hadin gwiwa masu amfani ta hanyoyi daban daban. Ta wannan dandali na ADB ne, kasar Sin ke yin cudanya tare da kasashen Afrika kan fasahohin da suka samu wajen neman bunkasuwa da kawar da talauci, kuma ta ba da kudin kyauta na dalar Amurka miliyan 314. Ya bayyana cewa, kasar Sin na bunkasa dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afrika a fili. Kuma tana taimakawa kasashen Afrika da zuciya daya, amma ba tare da ko wane irin sharadi ba. Kasar Sin na fatan kara yin mu'ammala da hada kai tare da kasashen duniya kan batun ba da taimako ga kasashen Afrika.

Kan maganar Darfur ta kasar Sudan kuma, Mr. Wen Jiabao ya nuna cewa, yanzu ana nan ana kan muhimmin mataki wajen warware matsalar shiyyar Darfur. Ya kamata kasashen duniya su ci gaba da yin shawarwari na zaman daidai wa daida tare da gwamnatin Sudan, kuma su kalubalan bangarori daban daban da abin ya shafa na Sudan da su aiwatar da shawarwarin siyasa tun da wuri, da kuma tabbatar da yarjejeniyar kawo zaman lafiya a shiyyar Darfur.

Mr. Kaberuka ya bayyana cewa, tun bayan da aka shigar da kasar Sin cikin ADB, ta yi ta kara ba da muhimmin taimako a kwana a tsahi wajen kau da talauci da rage basussuka, da dai sauran fannoni. (Bilkisu)