Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 19:16:42    
Shan ruwan inabi kullum zai ba da taimak ga lafiyar jiki

cri

Barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan ruwan inabi kullum zai ba da taimak ga lafiyar jiki, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, mazaunan birnin Dalian na kasar Sin masu fama da talauci sun samu taimako wajen jiyya.

Bayan da manazarta na kasar Birtaniya suka gudanar da bincike kan ruwan 'ya'yan itatuwa iri daban daban, sun gano cewa, sabo da yawan sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant da ke cikin ruwan inabi mai launin shuni yana da yawa, shi ya sa ya fi ba da taimako ga lafiyar jikin dan Adam idan an kwatanta shi da na sauran ruwan 'ya'yan itace.

A ran 15 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, jami'ar Glasgow ta kasar Birtaniya ta bayar da sanarwar cewa, manazarta na jami'ar sun gudanar da bincike kan ruwan 'ya'yan itace irin na 13. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, yawan sinadarin antioxidant da ke cikin ruwan inabi mai launin shuni yana da mafi yawa. Kuma ruwan apple da ruwan 'ya'yan itatuwa masu tsami sun zo na biyu da na uku. Kuma yawan irin wannan sinadari da ke cikin ruwan lemo kadan ne.

Sinadarin antioxidant yana taka muhimmiyar rawa wajen kare jikin dan Adam daga illar da free redicals ta yi masa, wato yana iya hana saurin tsufa da rage hadarin kamuwa da sankara da cututtukan zuciya ta hanyar hana free redicals, wanda ya kasance wani irin kwaya ce da ke lalata kwayoyin jikin dan Adam.

Furofesa Allen Klose da ya kula da binciken ya ba da shawarar cewa, ya fi kyau a hada ruwan inabi mai launin shuni da ruwan apple da kuma ruwan 'ya'yan itatuwa masu tsami tare a sha, wanda zai ba da taimako sosai ga lafiyar jiki.

A kwanan nan, manazarta na kasar Italiya sun ba da rahoto a kan mujallar ciwon sankara ta kasa da kasa, inda suka nuna cewa, rage yawan shan giya, da kara shan madara da cin danyun 'ya'yan itatuwa za su iya rage hadarin kamuwa da sankarar hanta.

Kuma rahoton ya bayyan cewa, bayan da manazarta na cibiyar nazarin sankara ta kasar Italiya suka gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci, sun gano cewa, lokacin da aka daina shan giya, kuma aka kara shan madara da kindirmo a ko wace rana, to, yiyuwar kamuwa da sankarar hanta za ta ragu da kashi 78 bisa dari idan an kwatanta da sauran mutane. Haka kuma idan an tsaya tsayin daka kan cin danyun 'ya'yan itatuwa a ko wace rana, to, yiyuwar kamuwa da sankarar hanta za ta ragu da kashi 52 bisa dari.

Sabo da haka manazarta sun bayyana cewa, cin abinci da kuma shan gida kamar yadda ya kamata zai iya rage hadarin kamuwa da sankarar hanta.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, mazaunan birnin Dalian na kasar Sin masu fama da talauci sun samu taimako wajen jiyya.