Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 18:48:33    
Kasar Sin na fatan yin cudanya da koyi da juna tare da kasashe mambobin ADB kan fasahohin da suka samu

cri

Yau 15 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Jiang Yu ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin na fatan yin amfani da damar shirya taron shekara-shekara na majalisa a birnin Shanghai da bankin raya kasashen Afrika, wato ADB za ta yi, za ta sa himma domin yin cudanya da koyi da juna tare da kasashe mambobi na ADB kan fasahohin neman bunkasuwa da suka samu, ta haka za a sa kaimi ga hadin kan tattalin arziki da ciniki a dukan fannoni a tsakanin Sin da Afrika.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, madam Jiang Yu ta ce, za a shirya taron shekara-shekara na majalisar ADB na shekarar 2007 daga ran 16 har zuwa ran 17 ga wata a birnin Shanghai, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ke sa himma domin nuna goyon baya ga shirya taron shekara-shekarar da ADB zai shirya, shi ne, domin goyon bayan ADB da ya ba da taimako sosai kan ayyukan kau da talauci da neman bunkasuwa a babban yankin Afrika. (Bilkisu)