Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 23:03:40    
Ina halartar taron shekara-shekara na majalisar Bankin raya Afrika, wato ADB na shekarar 2007

cri

Yau ranar 14 ga wata a birnin Shanghai, na samu damar yin hira da Dr.Bamanga Tukur?wanda ya kasance shugaban Business Round table ta Afirka kuma shugaban Nepad Business Group, wanda kuma ya yi jagoran kungiyar bankin raya kasa ta Afirka, wato bankin ADB, zuwa birnin Shanghai don halartar taron shekara shekara na bankin, wanda za a bude a jibi ran 16 ga wata.

Daga ranar 16 zuwa 17 ga watan nan da muke ciki, za a yi taron shekara shekara na bankin raya kasa ta Afirka a birnin Shanghai wanda ya kasance cibiyar tattalin arziki ta Sin. A yayin da muke tabo magana a kan me ya sa bankin ADB ta zabi birnin Shanghai na kasar Sin ta yi wannan taron shekara shekara nata, Dr.Bamanga Tukur ya ce, a cikin 'yan shekarun baya, dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ta karu sosai, musamman bayan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka da aka yi a shekarar da ta gabata a birnin Beijing, shugabannin kasashen Afirka masu dimbin yawa sun halarci taron, wanda ya kasance wani kasaitaccen taron da ba a taba yi ba ko a Amurka ko a Turai, sabo da haka, bankin raya Afirka ta ga bai kamata ta zauna ta yi shiru ba, shi ya sa ta zabi kasar Sin wajen yin wannan taronta na shekara shekara, don hada masu yin kasuwanci na Afirka da na Sin wuri daya, ta yadda za su kawo bunkasa hanyar ciniki da ke tsakaninsu.

Amma a yayin da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka ke ta ingantuwa, wasu sun fito sun ce, mulkin mallaka ne Sin take yi a Afirka. Game da wannan furuci, Dr.Bamanga Tukur ya ce, Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a Afirka ba, tana son dangatakar tattalin arziki tare da kasashen Afirka daga ko wane level, daga kauyuka zuwa birane. Ya ci gaba da cewa, Sin da Afirka ko wacensu ta yi moriya daga hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Afirka ma ta amfana kwarai daga hadin gwiwar, sabo da "in ba ta amfana ba, ko za a zo ne?", a cewarsa. Ya ce, in an duba, cinikin da ke tsakanin Sin da Afirka dinga karuwa take yi, har ma "ko wace rana ta fi ranar da ta wuce, ko wane wata ya fi watan da ya wuce, kuma ko wace shekara, ta fi shekarar da ta wuce", sabo da kowa na samun albarka.

Daga karshe, yayin muke neman ra'ayinsa kan makomar hadin gwiwar tattalin arziki da ke tsakanin Sin da Afirka, ya ce, zai karu kwarai da gaske, kuma ya yi fatan za a dinga yin irin wannan cudanya a tsakani, don a fahimci juna. Ya ce, "kamar mutane biyu za su yi aure, lokacin da suka yi sabo sabo, ba su gane juna sosai ba, amma suna daure gida daya, suna abu guda, to, za su fara gane hankali, kuma abin da za su yi zai karu zai kyautata."(Lubabatu)