Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 18:42:21    
Kasashe daban daban na Afirka suna fatan gama kai da hukumomin kudi na kasar Sin

cri

A ran 13 ga wata a birnin Shanghai, bi da bi ne, jami'ai da shugabannin bankunan da ke jiran halartar taron shekara-shekara na majalisar Bankin raya Afrika, wato ADB na shekarar 2007 suka bayyana cewa, suna fatan gama kai da hukumomin kudi na kasar Sin ciki har da bankin raya kasa na Sin, kuma suna son more kyakkyawan sakamakon da hukumomin kudi na kasar Sin suka samu a kan tattara kudi da amfani da kudi wajen raya kasa.

Wani jami'in ma'aikatar kudi da tsara shiri da kuma bunkasa tattalin arziki ta kasar Uganda Mr Caleb Akandwanaho ya ce, bankin raya kasa na Sin da ke da jarin da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 300 da kuma kyakkyawan sakamako wajen yin amfani da kudi wajen raya kasa, yana iya taimakawa kasashen Afirka a fannoni da yawa.

Ban da shi kuma, babban manajan bankin raya kasa na Kenya da kuma babban jami'in zartaswa na bankin gine gine na kasar Zimbabuwei su ma sun yi fatan gama kai da hukumomin kudi na kasar Sin.(Danladi)