Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 18:48:14    
Kasar Sin tana son hada kai da kasashen duniya wajen sa kaimi kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Darfur

cri
Ran 8 ga wata, a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Jiang Yu ta bayyana cewa, a cikin halin da muke ciki a yanzu, a lokacin da bangarorin da abin ya shafa suke tafiyar da aikin siyasa a yankin Darfur na kasar Sudan, a waje daya kuma, ya kamata bisa tushen yin shawarwari cikin adalci ne a dauki matakai don aiwatar da shirin da tsohon babban sakataren Majalsiar Dinkin Duniya Kofi Annan ya gabatar, a maimakon daukar ko wane iri mataki da zai tsananta halin da ake ciki, bangaren Sin yana son ci gaba da gama kansa da kasashen duniya wajen sa kaimi kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Darfur.

A lokacin da take amsa tambayoyin da manema labaru suka yi mata, madam Jiang ta ce, bangaren Sin ya bayyana matsayinsa kan batun Darfur a bayyane, ya kuma taka rawa mai yakini a kan daidaita batun. Kasar Sin tana shiga tsakanin bangarorin da abin ya shafa don shawo kansu wajen daidaita wannan batu cikin lumana ta hanyar yin shawawari da tattaunawa cikin adalci. Sa'an nan kuma, kasar Sin tana shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a Sudan.

Kazalika kuma, don biyan bukatar bangarorin Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa, yanzu gwamnatin Sin ta tsai da kudurin tura sojoji masu injiniya zuwa Darfur na Sudan, wadanda za su shiga ayyuka na mataki na 2 wajen aiwatar da shirin da Mr. Annan ya gabatar. (Tasallah)