Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-01 21:32:27    
Hanyar zaman rayuwa maras kyau za ta iya yin illa ga matasa da yara wajen karbar isashen sinadarin Calcium

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, hanyar zaman rayuwa maras kyau za ta iya yin illa ga samari da yara wajen karbar isashen sinadarin Calcium, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan ayyukan jiyya na unguwannin birnin Beijing.

A kwanan nan, kwamitin kula da labaran abinci na kasa da kasa, wani asusun da ke birnin Washington na kasar Amurka ya ba da rahoton cewa, hanyar zaman rayuwa maras kyau tana iya yin illa sosai ga wasu matasa da yara na kasar Amurka wajen karbar sinadarin calcium.

Kuma rahoton ya bayyana cewa, calcium wani muhimmin sinadari ne da ya zama wajibi ga yara lokacin da suke girma. Ko da yake ana iya samun magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sinadarin calcium iri iri yanzu, amma fiye da rabin matasa da yawa na kasar Amurka ba su samu isashen calcium da suke bukata a ko wace rana ba. Dalilin da ya sa haka shi ne hanyar zaman rayuwa maras kyau. Kuma a cikin rahoton, an ruwaito kididdigar bincike da ma'aikatar aikin gona ta Amurka ta bayar, cewa a cikin matasa da shekarunsu ya kai 12 zuwa 19 da haihuwa, mata da yawansu ya kai kashi 14 cikin dari da kuma maza da yawansu ya kai kashi 36 cikin dari kawai sun samu isashen sinadarin calcium.

Ban da wannan kuma rahoton yana ganin cewa, hanyoyin zaman rayuwa da suke iya yin illa ga matasan Amurka wajen karbar sinadarin calcium su ne cin kayayyakin kwalama wato fastfood, da shan lemon sosai, da rage kiba da matasa mata su kan yi idon rufe, da yin amfani da na'urar kwamfuta cikin dogon lokaci, da kuma rashin motsa jiki yadda ya kamata da dai sauransu.

Bugu da kari kuma rahoton ya nuna cewa, rashin samun isashen sinadarin calcium zai iya yin illa ga girman matasa. Kuma lokacin da suka tsufa, matasan da ba su samun isashen calcium sun fi saukin kamuwa da cutar kashi da ake kiranta "Osteoporosis", da hauhawar jini, da toshewar hanyoyin jini da kuma cutar sukari.

Sabo da haka hukumar nazari kan kiwon lafiya ta kasar Amurka ta ba da shawarar cewa, ya kamata yara da matasa da shekarunsu ya kai 9 zuwa 18 da haihuwa su karbi sinadarin calcium na miligram 1300 a ko wace rana. Haka kuma hukumar ta nuna cewa, yara da matasa su kan yi girma sosai lokacin da shekarunsu ya kai 9 zuwa 18 da haihuwa. Haka kuma halin lafiyar jiki da suke ciki a wannan lokaci ya kan taka rawa ga lafiyar jikinsu a duk rayuwarsu, shi ya sa suke bukatar karbar isashen sinadarin calcium.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan ayyukan jiyya na unguwannin birnin Beijing. Game da mutanen da ke da zama a birane, idan sun kamu da cututtuka, su kan je manyan asibitoci domin ganin likita. Amma kullum akwai nisa tsakanin manyan asibitoci da kuma unguwannin mazauna, kuma ana iya samun masu kamuwa da cututtuka da matukar yawa a wadannan asibitoci, ban da wannan kuma, kudin ganin likita a asibitocin suna da tsada. To, yaya za a iya warware wadannan matsaloli? An yi bincike a wannan fanni ta salon da ake bi a 'yan shekarun nan da suka gabata na yin jiyya a unguwannin birnin Beijing. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani a kan batun.