Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 16:07:30    
Bangaren Sin ya bayyana matsayinsa kan batun Darfur

cri
A ran 29 ga wata, Song Aiguo, shugaban sashen kula da harkokin Asiya da Afirka na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin wanda ya je birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya domin halartar taron ministocin kasashen da ke da nasaba da batun Darfur na kasar Sudan ya nuna cewa, bangaren Sin yana fatan bangarori daban daban za su iya kiyaye kyakkyawan masoma wajen warware batun Darfur, da kuma sa kaimi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya da kuma yunkurin siyasa na shiyyar Darfur.

Lokacin da yake ba da jawabi a gun taron a ran nan, Mr. Song ya bayyana matsayin bangaren Sin wajen warware batun Darfur, da kuma ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta yi domin warware batun yadda ya kamata. Haka kuma ya yi kira ga kasashe daban daban da su samar da taimakon jin kai ga shiyyar Darfur domin kyautata halin jin kai da shiyyar ke ciki, ta yadda za a iya tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa tun da wuri. Ban da wannan kuma ya bayyana cewa, bangaren Sin yana son ci gaba da bayar da gudummowarsa wajen warware batun Darfur yadda ya kamata.(Kande Gao)