Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-30 09:37:05    
An goyi bayan shirin tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a gun taro kan batun Darfur

cri

Taron ministoci kan batun Darfur na kasar Sudan da aka yi a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya ya bayar da sanarwa a ran 29 ga wata, inda ya nuna goyon baya ga shiri na mataki na uku da Kofi Annan, tsohon babban sakataren MDD ya gabatar wanda aka amince da shi kan jibge sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da na kungiyar tarayyar Afirka a shiyyar Darfur.

Wakilan da suka zo daga kasashe zaunannen membobi biyar na kwamitin sulhu na MDD da kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar tarayyar Turai da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da kuma wasu kasashen da ke shiyyar sun halarci taron. A gun taro na kwanaki biyu, masu halartar taron sun mai da hankulansu sosai kan batun Darfur, kuma sun yi kira ga bangarori masu gwagwarmaya da juna da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar yaki, da daina ayyukan nuna gaba ga juna nan da nan, da kuma daina kai farmako ga masu ba da taimakon jin kai da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka nan da nan.

Wakilin kasar Sin ya yi bayani a gun taron, cewa bangaren Sin yana fatan bangarori daban daban za su iya kiyaye kyakkyawan masoma wajen warware batun, da kuma sa kaimi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya da kuma yunkurin siyasa na shiyyar Darfur.(Kande Gao)