Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 15:30:33    
Sabunta: Firayim minista Wen Jiabao ya yi jawabi a majalisar dokoki ta Japan

cri

Ran 12 ga wata da safe, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin da ke ziyara a kasar Japan ya yi jawabi mai lakabi haka 'Domin zumunci da hadin gwiwa' a cikin majalisar dokoki ta Japan, ta haka ya zama kusan Sin na farko da ya yi jawabi a zauren majalisar dokoki ta Japan yau da shekaru 22 da suka wuce.

A cikin jawabinsa, Mr. Wen ya nuna cewa, yau da shekaru 35 da kasashen Sin da Japan suka komar da dangantakar da ke tsakaninsu yadda ya kamata, kasashen 2 sun sami babban ci gaba wajen raya huldarsu, jama'arsu sun ci gajiya sosai. Hada kai a tsakanin Sin da Japan zai kawo musu alheri, amma yin gwagwarmaya a tsakaninsu zai kawo musu illa, tabbatar da sada zumunta a tsakanin zuriyoyinsu yana dacewa da ci gaban tarihi da kuma burin jama'arsu duka, haka kuma buri ne na kasashen Asiya da gamayyar kasashen duniya.

Ya kara da cewa, a matsayinsu na muhimman kasashe na Asiya da na duniya, huldar da ke tsakanin Sin da Japan ta ba da babban tasiri kan Asiya har ma duk duniya, shi ya sa kamata ya yi kasashen 2 su kara taimakon juna da hada kansu, su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabashin Asiya tare, da kuma sa kaimi kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen yankin da suke ciki da himmantuwa kan farfado da Asiya.

Bayan da ya ba da jawabi, Mr. Wen ya gana da shugaban majalisar wakilai ta Japan Youhei Kono da shugabar majalisar dattijai ta Japan madam Chikage Ogi daya bayan daya. A gun ganawar da ya yi, Mr. Wen ya bayyana cewa, bin ka'idojin da ke cikin 'sanarwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Japan' da sauran takardun siyasa 2 da cika alkawarin da abin ya shafa da kuma daidaita muhimman batutuwan da ke jawo hankula a fannonin tarihi da Taiwan da dai sauransu dukkansu suna da matukar muhimmanci ta fuskar raya huldarsu. Kamata ya yi bangarorin 2 su mai da hankali kan halin da suke ciki wajen raya huldarsu, su kawar da cikas don kiyaye hali mai kyau da aka samu a sakamakon namijin kokarin da ake yi.

A nasa bangaren kuma, Mr. Youhei Kono ya ce, 'yan siyasa na Japan da Sin suna daukar nauyin kiyaye moriyar jama'arsu bisa wuyansu. Yana fatan bangarorin 2 za su kara yin tattaunawa a tsakaninsu da kara fahimtar juna da kuma sa kaimi kan yin hadin gwiwa. Madam Chikage Ogi ta ce, bunkasuwar tattalin arzikin Sin ta kawo wa Japan zarafi. Majalisar dattijai ta Japan tana fatan za ta kara yin mu'amala da tattaunawa da majalisar dokokin kasar Sin da kuma zabura wajen hada kan kasashen 2 a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki.(Tasallah)