|
|
 |
 |
| Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
| (GMT+08:00)
2007-04-11 18:22:13
|
 |
|
Firayin ministan kasar Sin ya fara yin ziyara a kasar Japan
cri
|
 Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Japan Abe Shinzo ya yi masa ne, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya isa birnin Tokyo domin fara yin ziyarar aiki a kasar Japan. Wannan ne karo na farko da firayin ministan kasar Sin ya kai wa kasar Japan ziyara bayan shekaru 7 da suka wuce.
A cikin jawaninsa da ya bayar a filin jirgin sama na Tokyo, Mr. Wen ya bayyana cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Japan. Yanzu yunkurin kyautata da raya dangantakar da ke tsakaninsu yana da muhimmiyar dama. Makasudin wannan ziyararsa shi ne kara amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa hadin guiwa irin ta moriyar juna da habaka yin musanye-musanye na sada zumunta domin ciyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan gaba cikin hali mai dorewa a cikin dogon lokaci mai zuwa. Yana fatan za a kai dangantakar makwabtaka irin ta sada zumunta da ke tsakanin Sin da Japan har wani sabon mataki ta wannan ziyarar da yake yi a Japan. (Sanusi Chen)
|
|
|