Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-11 18:03:14    
Wen Jiabao ya ba da jawabi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Korea ta Kudu

cri

A ran 11 ga wata da tsakar rana, a birnin Seoul, babban birnin kasar Korea ta Kudu, farayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya ba da jawabi ga mutanen da ayyukansu ke shafar tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Korea ta Kudu, inda ya gabatar da shawarwari hudu kan inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya, kuma yana fatan za a iya sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a wannan fanni ta kokarin da suke yi. A ran nan kuma firayim minista Wen ya gana da shugaban majalisar dokoki ta kasar Korea ta Kudu Lin Chae Jung.

A cikin jawabinsa, firayim minista Wen ya gabatar da cewa, ya kamata bangarorin Sin da Korea ta Kudu su ci gaba da habaka girman cinikayya, da kara zuba jari ga juna, da inganta hadin gwiwarsu a fannin kimiyya da fasaha, da kuma sa kaimi ga hadin kai wajen yin nazari kan shiyyar cinikayya maras shinge ta kasashen biyu.

Lokacin da yake ganawa da Jim Chae Jung, shugaban majalisar dokoki ta Korea ta Kudu, firayim minsita Wen ya bayyana cewa, kasashen Sin da Korea ta Kudu su muhimman kasashe ne da ke arewa maso gabashin Asiya. Bangaren Sin yana son hadin gwiwa tare da bangaren Korea ta Kudu wajen yin namijin kokari kan kara raya dangantakar abokantaka ta hadin kai tsakaninsu daga dukkan fannoni.(Kande Gao)