Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-11 09:55:23    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (04/04-10/04)

cri

Ran 9 ga wata,a hukunce ne kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya fara aikin zaben iyalan wasannin Olimpic domin su zo birnin Beijing yawon shakatawa a duk fadin duniya.Bisa mataki na farko,za a tattara `yan takara a duk fadin duniya ta hanyar yin amfani da tashar internet ta hukuma ta kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing wato www.beijing2008.cn, daga baya kuma masu amfani da internet za su jefa kuri`u,a karshe dai za a zabi iyalai biyar daga kasar Sin da iyalai biyar daga kasashen waje saboda su zama `iyalai na wasannin Olimpic`.Wadanda za su ci nasara za su zo nan birnin Beijing domin hallartar ayyuka a jere da za a shirya musamman dominsu a watan Agusta na bana.

Ran 7 ga wata,aka kammala gasa ta tsahar kasar Amurka ta gasar cin kofin duniya ta wasan bindigar `rifle` da na bindigar libarba wato `pistal`,a gun gasar da aka yi a wannan rana,`dan wasa daga kasar Sin Lin Zhongzai ya samun lambar zinariya ta gasar bindigar `rifle` ta mitoci 50 ta maza,`dan wasa daga kasar Sin daban Shi Xinglong ya samun lambar tagulla ta gasar,tashar kasar Amurka ita ce tasha ta farko ta gasar cin kofin duniya ta wasan bindigar `rifle` da na bindigar libarba ta wannan shekara,gaba daya kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samun lambobin zinariya 4 da na azurfa 4 da na tagulla 3,wato lambobin yabo da ta samu sun fi yawa.

Kwanakin baya,shahararren `dan wasan tsinduma cikin ruwa na kasar Sin Tian Liang ya sanar da cewa zai yi ritaya,a wannan shekara,Tian Liang yana da shekaru 28 da haihuwa,a cikin shekaru 10 da suka shige,an mayar da shi a matsayin daya daga cikin `yan wasan tsinduma cikin ruwa mafi nagarta a duniya,sau tarin yawa ne ya taba samun lambobin zinariya a gun gasannin cin kofin duniya na wasan iyo,musamman ma a gun taron wasannin Olimpic na Sydney na shekarar 2000 da na Athens na 2004,Tian Liang ya zama zakaran wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali na mita 10 sau biyu.(Jamila Zhou)