Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-09 15:24:56    
Shugaban kasar Sudan ya gana da manzon musamman na gwamnatin kasar Sin Mr. Zhai Jun

cri
Jiya 8 ga wata, shugaba Omar Hassan Ahmed Al-bashir na kasar Sudan, ya gana da manzon musamman na gwamnatin kasar Sin, kuma mai ba da taimako na ministan harkokin waje Mr. Zhai Jun, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Sudan da Sin, da matsalar shiyyar Darfur, da kuma sauran batutuwa.

Mr. Al-Bashir ya yi yabo sosai ga kyakkyawar dangantakar hadin kai da ke tsakanin Sudan da Sin, kuma ya bayyana cewa, gwamnatin Sudan ta amince da shirin Annan bisa manufa, tana son yin shawarwari da tabbatar da wannan tare da M.D.D. da kungiyar tarayyar kasashen Afrika, wato AU. Kasar Sudan tana fatan tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a shiyyar Darfur tun da wuri.

Mr. Zhai Jun ya bayyana cewa, ziyarar aiki da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi a kasar Sudan cikin nasara a watan Feburairu na shekarar da muke ciki, ta zuba sabon karfi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Sudan. Yana fatan kasar Sudan za ta kara sassauta matsayinta a kan shirin Annan, kuma za ta ci gaba da kyautatta halin da ake ciki a shiyyar Darfur a fannonin jin kai da zaman lafiya, da kuma kara saurin yunkurin siyasa a shiyyar. Kasar Sin tana son ba da taimako bisa manyan tsare-tsare, domin tabbatar da zaman lafiya da zaman karko, da kuma samun bunkasuwa a shiyyar Darfur tun da wuri.

Mr. Zhai Jun da kuma 'yan rakiyarsa sun isa birnin Khartoum ne a ran 6 ga wata, kuma za su yi ziyarar da za a shafe kwanaki 4 ana yinsa a kasar Sudan. (Bilkisu)