Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-06 18:50:06    
Kasar Sin na kokari wajen rage gibi da ke tsakanin masu arziki da matalauta don sa kaimi ga raya zaman al'umma mai jituwa

cri

A sakamakon ci gaba mai dorewa da ake ta samu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, yawan kudin shiga da jama'ar Sin ke samu ma ya karu cikin sauri. Amma gibi da ke tsakanin masu arziki da matalauta ma ya habaka. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bangarori daban daban na jama'ar kasar suna ta mai hankali sosai ga matsalar gibi da ke tsakanin masu arziki da matalauta. Yanzu, za mu bayyana muku matakai da gwamnatin kasar ta dauka don rage irin wannan gibi.

Bisa kidayar da cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum ta kasar Sin ta yi, an ce, kashi 20 cikin dari na yawan kudin shiga da mutanen kasar ke samu ya ninka kimanin sau 18 bisa na wadanda ke samu albashi mafi karanci.

Ba ma kawai wannan matsalar tattalin arziki ba ce, har ma shi wata matsala ce da ta shafi zaman al'amma cikin daidaici, kuma yana kawo tasiri ga dukiyoyi da ake rarraba wa jama'a cikin daidaici da ci gaba mai dorewa da ake samu wajen bunkasa tattalin arziki.

A kasar Sin, yawan kudin shiga da manoma ke samu ya yi kasa da na mazaunan birane sosai. Don neman daidaita wannan matsala, tun daga shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai daban daban wajen bai wa manoma taimkon kudi don sayen ire-iren amfanin gona masu kyau da injunan noma na zamani da sauransu, ta yadda za su kara samun kudin shiga. Haka kuma yawan kudin shiga da mazaunan birare da garuruwa na kasar ke samu ma ya sha bamban sosai. Don haka gwamnatin kasar tana mai da hankali sosai wajen ba da taimako ga mazaunan birare da garuruwa wadanda ke fama talauci sosai.

Tsoho Yao Rugen mai shekaru sama da 60 da haihuwa wani matalauci ne da ke zama a birnin Changchun na lardin Jilin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, Shi nakasasshe ne, yau da 'yan shekaru da suka wuce, an sallame shi daga wani ma'aikata da aka rufe shi. Yanzu, hukumar wurinsa ya kan ba shi kudin Sin Renminbi Yuan sama da 200 a ko wane wata don zaman rayuwarsa. Tsoho Yao Rugen ya bayyana cewa, "ban da yawan kudin da nake samu a ko wane wata, kuma na kan iya samun kudin taimako Yuan sama da 1,600 daga hukumar a ko wace shekara don daumama daki a yanayin dari. Sa'an nan hukumar ta kan ba ni taimkon kudi Yuan sama da 100 a ko wane wata don hayar gida. A kwanakin baya ba da dadewa ba, hukumar ta ba ni wani katin asibiti, wanda zan iya amfani da shi wajen ganin likita ba tare da biyan kudin rajista ba, ka zalika inda an kwantar da ni asibit ma, ba zan biya kudin gado ba."

Yayin da gwamnatin kasar Sin ke ba da taimakon kudi ga mutane masu samun albashi kadan, kuma tana mai da hankali sosai wajen daidaita kudin shiga da jama'a ke samu ta hanyar buga haraji. Malam Wang Li, mataimakin shugaban babbar hukumar kula da harkokin haraji ta kasar Sin ya ce, "a shekarar bara, yawan kudin shiga da ko wane mutum ke samu, wanda kuma ba a buga haraji a kansa ya karu zuwa kudin Sin Yuan 1,600 a ko wane wata. Bisa kididdigar da aka yi ba sosai ba, an ce, ta haka yawan mutane da ba su biya irin wannan harji ya karu sama da miliyan 20. Lalle wannan ya kawo amfani ga kare zaman al'umma cikin daidaici da raya zaman al'umma mai jituwa."

Ko da yake kasar Sin ta sami sakamako mai kyau wajen rage gibi da ke tsakanin masu arziki da matalauta, amma duk da haka ya kasance da gibi a tsakaninsu. Malam Ma Kai, shugaban hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin ya ce, "wajibi ne, a dauki matakan tattalin arziki da dokoki don daidaita yawan kudin shiga da jama'a ke samu. A kara kyautata tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, kuma a yi kokari sosai don taimaka wa mazaunan birane da na kauyuka wajen kawar da wahalhalu da suke sha a fannin zaman rayuwa da harkokin samar da kayayyaki, musamman ma a rubanya kokari sosai wajen tallafa wa mutane masu fama da talauci a kauyuka." (Halilu)