Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 20:52:37    
Shugabannin Sin da Rasha sun halarci bikin bude 'shagalin nune-nune na kasar Sin'

cri

Ran 27 ga wata, a cibiyar nune-nunen kayayyaki ta Crocus da ke birnin Moscow, an bude 'shagalin nune-nune na kasar Sin', wanda shagali ne mafi girma da gwamnatin kasar Sin ta nuna kayayyakinta dangane da fannoni mafi yawa. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ke ziyara a kasar Rasha da kuma takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin bude shagalin cikin hadin gwiwa.

'Shagalin nune-nune na kasar Sin' na daya daga cikin muhimman ayyuka da gwamnatin Sin ta yi a gun bikin 'shekara don kasar Sin', wadda aka kaddamar da ita ba da jimawa ba, babban batun shagalin shi ne yin hadin gwiwa don cin nasara tare da samun bunkasuwa cikin jituwa. A cikin shiyyar nune-nune mai fadin murabba'in mita dubu 20, kamfanoni da hukumomi da kungiyoyi fiye da 200 daga birane da larduna 31 na babban yankin Sin da kuma yankunan musamman na Hong Kong da Macao sun nuna kayayyaki iri-iri har dubu 15 da hotuna fiye da dubu guda a fannoni 30 ko fiye, kamar su siyasa da tattalin arziki da ala'du da dai sauransu. Shagalin ya bayyana matsayin ci gaba na sana'o'i daban daban na kasar Sin.

A gun bikin bude shagalin, shugaba Hu ya yi jawabi, inda ya ce,'Shagalin zai nuna wa jama'ar Rasha dogon tarihin kasar Sin da nagartattun al'adunta, da ci gaban Sin a fannin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga duniya da raya kasa ta zamani, da kuma sakamako da yawa da Sin da Rasha suka samu daga wajen hadin gwiwarsu ta tattalin arziki da ciniki. Shagalin nune-nunen kasar Rasha da aka yi a kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar bara ya samar wa jama'ar Sin kyakkyawar alamar tunani. Na yi imani cewa, tabbas ne 'shagalin nune-nune na kasar Sin' zai zama wani kasaitaccen taro na yada zumuncin gargajiya da ke tsakanin jama'ar Sin da Rasha da kuma wani dandalin sa kaimi kan hada kansu.'

A shekarun baya da suka wuce, Sin da Rasha sun raya huldar tattalin arziki da ciniki yadda ya kamata a tsakaninsu, sun kuma zuba wa juna jari sosai bisa sikeli mai girma. A cikin jawabin da ya yi, shugaba Hu yana fatan bangarorin 2 za su yi amfani da muhimmiyar dama da suke samu, wato shirya bikin 'shekara don wata kasa' a tsakanin juna, su nemi tare kuma da raya sabbin fannonin hadin gwiwa. A yayin da suke hada kansu bisa sikeli mai girma, ya kamata su mai da hankulansu kan kyautata hadin gwiwarsu da daga matsayin hadin gwiwarsu, ta haka za su sa kaimi kan dangantakar hadin gwiwa da aminci da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon mataki, kazalika kuma za su kawo wa jama'arsu fa'ida.

An yi karin bayani cewa, nufin shirya 'shagalin nune-nune na kasar Sin' shi ne sa kaimi kan ingantattun masana'antu da kayayyaki na kasar Sin da su shiga cikin Rasha, shagalin zai zama dandamali ne wajen kara yin cudanya a tsakanin masana'antun kasashen 2 da habaka hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni. Shugaba Putin kuma yana fatan alheri sosai kan 'shagalin nune-nune na kasar Sin', a jawabin da ya yi, ya ce,''Shagalin nune-nune na kasar Sin' ya nuna mana sakamako mafi kyau da Sin ta samu daga wajen bunkasuwar tattalin arziki. Wannan ne dama mai kyau ga Rasha a fannin ganin sakamakon da Sin ta samu bayan da ta yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga duniya. Na yi imani cewa, ta wannan shagali ne, bangarorin 2 za su kaddamar da dimbin sabbin ayyukan hadin gwiwar fasaha da kawo albarka. Ina fatan cikakkiyar nasara za ta tabbata ga 'shagalin nune-nune na kasar Sin'.'

Bayan bikin bude shagalin, shugaba Hu da shugaba Putin sun kuma kai ziyara wajen shagalin.(Tasallah)