Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-27 18:10:33    
Shugabannin kasashen Sin da Rasha sun bude bikin "Shekara don kasar Sin" da aka fara yi a kasar Rasha

cri

A ran 26 ga wata a babban dakin taro na fadar Kremlin da ke birnin Moscow, babban birnin kasar Rasha, an shirya shagalin kaddamar da bikin "Shekara don kasar Sin" da za a yi a kasar Rasha. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Rasha da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci shagalin, inda suka bude wannan bikin "Shekara don kasar Sin".

Bisa alkawarin da shugabannin kasashen Sin da Rasha suka dauka, a shekara ta 2006, an yi bikin "Shekara don kasar Rasha" a kasar Sin. A shekarar da muke ciki, wato shekara ta 2007, za a yi bikin "Shekara don kasar Sin" a Rasha. Sabo da haka, a ran 26 ga wata da dare, shugabannin kasashen biyu sun bude wannan biki a babban dakin fadar Kremlin na birnin Moscow.

A gun shagalin kaddamar da bikin "Shekara don kasar Sin" da aka shirya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, "A shekarar da muke ciki, za mu shirya bikin 'Shekara don kasar Sin' a kasar Rasha. A gun wannan biki, za a shirya ayyuka kusan dari 2 wadanda za su shafi siyasa da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da al'adu da zaman al'ummar Sin da dai sauransu. Muna fatan za mu iya bayyana wa jama'ar Rasha al'adu da tarihin kasar Sin da tarihin yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen waje na kasar Sin domin kara fahimtar juna da zumunta a tsakanin kasashen biyu da jama'arsu yayin da ake zurfafa hadin guiwa da musanye-musanye a tsakaninsu a fannoni daban-daban."

A cikin nasa jawabin, Mr. Putin ya ce, "Kudurin shirya bukukuwan shekara don wata kasa da shugaba Hu Jintao da ni muka tsaida yana da ma'anar da ke shafar dogon lokaci mai zuwa. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, wannan kuduri daidai ne, kuma yana kawo mana fifiko kwarai. Makasudin shirya irin wannan muhimman bukukuwa shi ne kara kyautata inganci da matsayin yin hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu. A waje daya kuma, za a iya kara fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu da tabbatar da dangantaka mai kyau da ke tsakaninsu ba tare da kasala ba ta irin wannan bukukuwa."

1 2