Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-27 14:53:29    
An shirya bikin bude shagalin 'shekarar Sin a Rasha'

cri

A ran 26 ga wata da dare, a fadar Kremlin ta birnin Moscow ta kasar Rasha, an shirya bikin bude shagalin 'shekarar Sin a Rasha'. Shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda yake ziyara a kasar Rasha da takwaransa na Rasha Mr Putin sun halarci bikin.

A gun bikin budewa, shugaba Hu ya bayar da wani jawabi cewa, ta aikace aikacen da aka shiry a lokacin shagalin 'shekarar Sin a Rasha', kasar Sin tana fatan cewa, za ta bayyana al'adu da tarihi na kasar Sin da kuma yunkurin yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya da kasar Sin take gudanarwa ga jama'ar kasar Rasha, haka kuma jama'ar kasashen biyu za su kara fahimtar juna da sada zumunci ga juna, kuma za a kara zurfafa hadin kansu a fannoni daban daban, ta yadda za a iya kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a tsakanin Sin da Rasha.

Mr Putin ya bayyana cewa, har kullum kasashen Sin da Rasha suna nuna abin koyi wajen kafa dangantakar daidaici da ta jituwa a tsakanin kasa da kasa. Bukukuwan kasa da bangarorin biyu suka yi ga juna sun samu nasarori da yawa, lallai wannan ya bayyana cewa, dangantakar abokantaka da ke tsakanin Sin da Rasha tana da kyakkyawar makoma.

A ran 26 ga wata da yamma, shugaban Hu Jintao ya yi shawarwari da Mr Putin. Bangarorin biyu sun bayyana cewa, dukkansu sun yarda da bin yarjejeniyar hadin kai ta zaman jituwa da makwabtaka a tsakanin Sin da Rasha, kuma sun zama abokai ga juna wato irin na hadin kai a fannin siyasa da moriyar juna a fannin tattalin arziki da yin kirkire-kirkire tare a fannin kimiyya da fasaha da zaman jituwa a fannin al'adu da kuma taimawakawa juna a fannin tsaro. Bayan shawarwarin da suka yi, shugabannin biyu sun daddale hadaddiyar sanarwa a tsakanin Sin da Rasha.(Danladi)