Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-26 18:15:24    
Hu Jintao ya isa birnin Moscow don fara ziyararsa a kasar Rasha

cri

A ran 26 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa birnin Moscow, babban birnin kasar Rasha ta jirgin sama na musamman domin fara yin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bikin bude bikukuwan 'shekarar kasar Sin a Rasha' da dai sauran aikace aikace, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa.

Sojojin nuna girmamawa da 'yan badujala na rundunar sojojin jiragen sama da na ruwa da kuma na kasa na kasar Rasha sun shriya biki a filin jirgin sama don maraba da zuwan shugaba Hu.

Kuma shugaba Hu ya ba da jawabi a rubuce a filin jirgin sama, cewa shekara ta 2006 wata muhimmiyar shekara ce ga kasashen Sin da Rasha wajen samun babban ci gaban dangantakar da ke tsakaninsu. Kuma bangarorin biyu sun yi amfani da damar shirya bikin "shekarar kasa" wajen sa kaimi ga ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha zuwa gaba bisa manyan tsare-tsare. Ban da wannan kuma Shugaba Hu ya bayyana cewa, bangaren Sin yana son hadin gwiwa tare da bangaren Rasha wajen aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa ta aminci tsakanin kasashen biyu domin kara fahimtar juna da kuma inganta zumuncin da ke tsakaninsu da jama'ar kasashensu, da kuma inganta hadin gwiwarsu a sabbin fannoni, ta yadda za su iya bayar da gudummowarsu waje kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa gaba daya a duk duniya. Bugu da kari kuma shugaba Hu ya yi imanin cewa, ta ziyarar da yake yi, za a bude wani sabon shafi wajen inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha da kuma zabura hadin gwiwa tsakaninsu.(Kande Gao)