Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-26 14:13:57    
Shugaba Hu Jintao ya bar Beijing domin kai ziyara a kasar Rasha

cri

Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, a ran 26 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bar Beijing ta jirginsa na musamman domin kai ziyarar aiki a kasar Rasha, kuma zai halarci aikace aikace da yawa, wadanda za su hada da bikin 'shekarar kasar Sin a Rasha' da kuma bikin bude taron nune-nunen kayayyakin Sin a Rasha da dai sauransu.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a lokacin ziyararsa, shugaba Hu zai gana da takwaransa na kasar Rasha da shugaban majalisar Duma da kuma firayin ministan kasar Rasha bi da bi, za su yi musanyar ra'ayoyinsu a kan yadda za a kara zurfafa dangantakar hadin kai da abokantaka bisa manyan tsare tsare a tsakaninsu da kuma lamuran kasa da kasa da shiyya shiyya da ke jawo hankulansu.

Shugabannin kasashen Sin da Rasha za su halarci bikin bude shagalin 'shekarar kasar Sin a Rasha', kuma za su ga shirye shiryen wasanni da shahararrun masu fasaha na kasar Sin za su yi.

Taron nune-nunen kayayyakin Sin a Rasha ya fi girma bisa matakin nune-nunen da aka yi a kasashen waje ta fuskar fannoni da yawa, wanda kasar Sin za ta shirya a ketare bisa matsayin kasa. Hukumomi kimanin 200 daga jihohin kasar Sin da Hongkong da Macao da sauransu wadanda yawansu ya kai 31 na kasar Sin za su halarci taron. A gun nune nunen, kamfanonin Sin da Rasha za su yi mu'amala da juna, ana kyautata zaton cewa, yawan kudin yarjejeniyoyin da za su daddale zai zarce dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 300.(Danladi)