Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 15:04:39    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(15/03-21/03)

cri

A kwanan baya, a birnin Shanghai na kasar Sin, a gun gasar fid da gwani ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin da aka shirya a cikin daki, 'yar wasa Zhang Yingning na kasar Sin, wadda shekarunta ya kai 17 kawai ta karya matsayin bajimta na Asiya a gun gasar tsallen gora ta mata a cikin daki.

Ran 17 ga wata da dare, a birnin Melborne na kasar Australia, an bude gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya a karo na 12. 'Yan wasa 2195 da suka zo daga kasashe da yankuna 173 na duniya sun shiga wannan gasa, yawan kungiyoyi da 'yan wasa masu halartar gasar ya karya matsayin bajimta a cikin tarihin wannan muhimmiyar gasar iyo. Kasar Sin ta aika da 'yan wasanta 104 zuwa wannan gasa don share fage ga taron wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekara ta 2008.(Tasallah)


1 2