 Jaridar People's Daily ta kasar Sin za ta ba da sharhi a gobe wato ran 16 ga wata, don murnar cin nasarar rufe taro na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC.
Sharhin ya bayyana cewa, a lokacin taron, 'yan majalisar sun aiwatar da nauyin da ke kansu a tsanake, sun ba da shawarwari, hakan ya nuna kuzari da karfi na majalsiar CPPCC, wadda ita kungiyar siyasa ce, kuma 'yan majalisar sun iya ba da shawarwari ta hanyar dimokuradiyya.

Sharhin ya kara da cewa, shekarar bana shekara ce mai muhimmanci a fannin aiwatar da tunanin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya daga dukan fannoni da gaggauta raya zaman al'ummar kasar gurguzu mai jituwa, haka kuma shekara ce da za a raya ayyukan majalisar CPPCC bisa ra'ayin fahimtar abubuwan da suka wuce a baya tare da yin marhabin da abubuwan da ke gaba, tare kuma da ra'ayin kirkire-kirkire. Ya kamata majalisar CPPCC ta taka rawa sosai, ta haka za ta ci sabbin nasarori a fannin sa kaimi kan ayyukan tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'ummar kasa irin na gurguzu, za ta kuma samar da kyakkyawan hali da sharadi domin babban taron wakilai na karo na 17 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.(Tasalah)
|