
Ran 13 ga wata, a nan Beijing, ministan 'yan kwadago da jin dadin jama'a ta kasar Sin Tian Chengping ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin na fuskantar hali mai tsanani a fannin samar da guraban aikin yi, nan gaba za ta dauki tsauraran matakai don daidaita wannan batu.

Mr. Tian Chengping ya fadi haka ne a gun taron manema labaru da aka yi domin taron shekara-shekara na majalisar dokoki ta kasar Sin. Ya kara da cewa, yawan mutanen da suka samu aikin yi ya karu da rarar miliyan 110 ko fiye a cikin garuruwa da birane a shekarar bara, wadda shekara ce da aka fi samun irin wadannan mutane. Amma kasar Sin na fuskantar babbar matsin lamba a fannin samar da guraban aikin yi nan da shekaru da dama masu zuwa, mutane suna gamuwa da hali mai tsanani wajen samun aikin yi.
Mr. Tian ya ci gaba da cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin samar da guraban aikin yi masu yakini, za ta kara kyautata da aiwatar da manufofin sa kaimi kan samar da guraban aikin yi a fannonin kudi da haraji da dai sauransu.(Tasallah)
|