Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-12 18:50:14    
Jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin

cri

Jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin tana birnin Chengdu, hedkwatar jihar Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Zeng Ming, mataimakin shugaban jami'ar ya gaya wa wakilinmu cewa, an kafa jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin ne a shekara ta 1951, kuma tana daya daga cikin jami'o'in kabilu na farko da aka kafa bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Ya zuwa yanzu, daliban da ke karatu a cikin jami'ar sun hada da dukkan kabilun kasar Sin. Kuma ya kara da cewa, "Wasu daliban da ke jami'ar sun zo daga kananan kabilu da ba su da yawan mutane, yawan mutane na irin wadannan kabilu bai fi dubbai ba. Ban da wannan kuma a cikin jami'armu, wata dabila ta kabilar Tajik da ake kiranta 'bakuwa daga dutsen kankara' daliba ce ta musamman, dalilin da ya sa na fadi haka shi ne sabo da ta kwashe lokaci mai tsawon fiye da wata guda tana zuwa jami'ar da kafarta."

Haka kuma Mr. Zeng ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru fiye da 50 bayan da aka kafa jami'ar kabilu ta kudu maso yammacin kasar Sin, an riga an horar da kwararrun da yawansu ya zarce dubu 90 a fannin sana'o'i iri daban daban, ciki har da mai babban digiri na Doctor na farko na kabilar Tibet da na kabilar Qiang, da shahararrun kwararru da masana a kan harkar sana'o'i daban daban masu yawa, wadanda suke bayar da gudummuwa sosai ga bunkasuwar yankunan kananan kabilun kasar Sin.

Kowa ya sani, harsunan kabilun kasar Sin suna da yawa, kuma al'adun gargajiya na kabilun sun sha bamban da na sauran. Idan an hada daliban da suka zo daga kabilu 56 na kasar Sin tare, ko yaya za su iya fahimtar juna? kuma ko ta yaya za su iya taimaka wa juna wajen samun ci gaba a fannin karatu?

1 2