
Yanzu ana yin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin a nan birnin Beijing. Ran 9 ga wata, daya bayan daya shugabannin kasar Sin Mr. Hu Jintao, da Mr. Wen Jiabao, da kuma Mr. Jia Qinglin da dai sauransu, suka yi tattaunawa tare da 'yan majalisun wakilan jama'ar kasar, wadanda suke fito daga shiyyar mai ikon aiwatar da kanta ta kabilar Zhuang ta jihar Guangxi, da kuma jihar Zhejiang, da kuma sauran wurarre, kan daftarin dokar mallakar dukiyoyi, da kuma shirin sabuwar dokar buga haraji kan kudin riba na masana'antu, bayan haka kuma, sun bayyana ra'ayoyi kan batun kara saurin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma ta yankunan kananan kabilu, da dai sauran batuttuwa.
A lokacin da ya ke tattaunawa tare da kungiyar wakilai ta jihar Guangxi, shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kamata jihar Guangxi ta yi amfani da sabuwar damar hadin kai a tsakanin shiyya-shiyya, ta sa himma domin halartar aikin raya yankin cinikayya na 'yancin kai na Sin da ASEAN, da kuma sauran hadin kai a tsakanin shiyyoyi da dama, don karfafa bude kofa ga kasashen waje, da hadin kai na samun moriyar juna, kuma ta mai da hankali kan warware matsalar zaman rayuwar jama'a, da kara samar da aikin yi, da kyautatta tsarin tsaron zaman al'umma, da kuma kara saurin bunkasuwar sha'anin ba da ilmi da na kiwon lafiya.
Mr. Wen Jiabao ya halaci taron tattaunawa tare da kungiyar wakilan jihar Hainan da ke kudancin kasar Sin ta shirya, inda ya bayyana cewa, ya kamata Hainan ta mai da aikin kiyaye muhalli a matsayin farko wajen bunkasuwar tattalin arziki. Mr. Jia Qinglin kuma ya nuna cewa, ya kamata, a fahimci kan muhimman manufofi da abubuwan da ke cikin daftarin dokar mallakar dukiyoyi, da kuma shirin sabuwar dokar buga haraji kan kudin riba na masana'antu a tsanake. (Bilkisu)
|