
Yau a nan birnin Beijing, shugaban gwamnatin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, Mr.Ismail Tiliwaldi ya bayyana cewa, Xinjiang ta riga ta shiga zamanin saurin bunkasuwar harkokin tattalin arziki da na zaman al'umma.
A yayin da Mr.Ismail Tiliwaldi ke amsa tambayar da wakilinmu ya yi masa, ya ce, a shekarar bara, yawan GDP na Xinjiang ya karu da kashi 11.2%, wanda ba safai a kan samu irinsa ba a tarihi . An fara jerin wasu manyan ayyuka da ke shafar ruwa da sufuri da makamashi da dai sauransu ko kuma kammala su. Ban da wannan, Xinjiang ta yi ta kara samun masu yawon shakatawa da kamfanonin da ke zuba mata jari. A shekarar da ta gabata, akawi kamfanoni masu jarin waje 66 da suka yi rajista a Xinjiang, Xinjiang ta kuma karbi masu yawon shakatawa da yawansu ya kai dubu 350.(Lubabatu)
|