
Yau a nan birnin Beijing, shugaban gwamnatin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, Mr.Ismail Tiliwaldi ya bayyana cewa, sansanin horar da 'yan ta'adda na kungiyar Islama ta gabashin Turkistan da aka murkushe a jihar a watan Janairu na wannan shekara, yana da nasaba sosai da kungiyar Al-Qaeda.
Yayin da yake hira da manema labaru na gida da na waje a ran nan, Mr.Ismail Tiliwaldi ya ce, babban makasudin kungiyar Islama ta gabashin Turkistan shi ne neman kawo ta'addanci da baraka da kuma lalata tsaron kasar Sin. Ta'addanci babbar barna ce ga duniya, gamayyar kasa da kasa suna yaki da ta'addanci.(Lubabatu)
|