
Yanzu ana yin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin a nan birnin Beijing. Ran 8 ga wata, daya bayan daya shugabannin kasar Sin Mr. Hu Jintao, da Mr. Wu Bangguo, da Mr. Wen Jiabao, da kuma Mr. Zeng Qinghong, da dai sauran shugabannin kasar suka dudduba rahoton ayyukan gwamnatin tare da 'yan majalisar wakilan da suka fito daga birnin Chongqing, da jihar Jilin, da kuma sauran wurarre, kuma sun bayar da ra'ayoyi kan batutuwan kara saurin bunkasuwar gine-ginen sabbin kauyuka na gurguzu, da karfafa tsarin dokoki da sauransu.
Shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa nuna goyon baya ga sha'anin gona na zamani, da ayyukan kara yawan kudin shiga na manoma, da kuma gine-ginen kauyuka, kuma a juya hanyar bunkasuwar tattalin arziki a hakika, da warware matsalar zaman rayuwar jama'a, da kuma karfafa gine-ginen birane a duk fannoni.
Mr. Wu Bangguo ya kuma jaddada cewa, tilas ne a tsara dokokin shari'a bisa manufa kamar haka, wato mai da moriyar jama'a ta zama cibiyarta.
Mr. Wen Jiabao ya ce, ya kamata a ci gaba da karfafa manyan ayyuka a shiyyoyi masu fama da talauci, da kuma kara karfin bunkasa sana'o'in musamman, domin tsayawa kan yin ayyukan fama da talauci.(Bilkisu)
|