Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 21:46:19    
Shugabannin Sin sun halarci shawarwarin wasu kungiyoyi mahalartan taron NPC

cri
Yau a nan birnin Beijing, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugabannin kasar, Huang Ju da Wu Guanzheng da Li Changchun da kuma Luo Gan sun halarci shawarwarin kungiyoyin wakilai na birnin Shanghai da lardin Liaoning da jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da kuma birnin Tianjin, wadanda ke halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato NPC, inda kuma su bayar da ra'ayoyinsu dangane da magance cin hanci da tabbatar da akidar samun ci gaba ta hanyar kimiyya da kara karfin raya siyasar dimokuradiyya da dai sauran batutuwa.

Mr.Huang Ju ya jaddada cewa, bunkasa harkokin tattalin arziki da zaman al'umma ya dogara ne bisa karfin rukunin shugabannin da halayensu. Ya nemi da a kyautata da inganta tsarurruka da kuma gudanar da su yadda ya kamata, a kara inganta ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta Sin, a kara sa ido a kan muhimman shugabanni, ta yadda za a kawar da ayyukan cin rashawa daga asalinsu.

A yayin da yake sauraron jawaban wakilai dangane da bunkasa sabbin kauyuka irin na gurguzu da sa kaimi ga samar da aikin yi da dai sauransu, Mr.Wu Guanzheng shi ma ya bayar da ra'ayinsa dangane da kara sabunta tsarurruka da magance ayyukan cin hanci tun daga asali.(Lubabatu)