Mukadashin sakataren kwamitin birnin Shanghai na jam'iyyar kwaminis ta Sin kana kuma magajin birnin, Mr.Han Zheng ya bayyana a yau ranar 7 ga wata cewa, Shanghai za ta kara tafiyar da harkokin mulki a fili, kuma za ta sa ido sosai a kan yadda ake tafiyar da harkokin mulki.
Mr.Han Zheng ya ce, Shanghai za ta kara karfin bunkasa tsarin harkokin mulki, musamman ma a fannin tafiyar da harkokin mulki bisa doka. A sa'i daya kuma, za ta tafiyar da harkokin mulki a fili, za ta sa ido sosai a kan yadda ake tafiyar da harkokin mulki, don kada a tafiyar da harkokin mulki yadda aka ga dama.(Lubabatu)
|