Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 17:10:22    
Wani mashahurin mutumin kasar Sin mai suna Sun Yat-sen

cri

An haifi Sun Yat-sen a wani gidan manoma a shekarar 1866 a lardin Kwangdong da ke kudancin kasar Sin. Iyayensa suna aikin noma, dukkan mutanen iyalinsu sun yi zaman rayuwarsu na yau da kullum a cikin wata bukka kawai, sun yi fama da talauci sosai, bai taba sanya takalmi ba sai lokacin da ya girma har zuwa shekarunsa na haihuwa ya wuce goma , amma a wurin da ke da manyan tsaunuka, ya yi tafiya ba tare da sanya takalmi ba, to tabbas ne ya sha wahaloli da yawa. Ba sau daya ba ba sau biyu ba Mr Sun Yat-sen ya gaya wa matarsa Son Qingling cewa, tun daga lokacin da yake karami kuma yake fama da talauci, ya yi niyya cewa, bai kamata ba manoman kasar Sin su yi fama da talauci cikin dogon lokaci, ya kamata yaran kasar Sin su sami takalmi tare da samun abinci. Amma abin bakin ciki shi ne, a cikin duk lokacin da yake da rai a duniya, bai sami damar ganin abun da ya yi fatan gani ba .

A zamanin da Mr Sun Yat-sen yake zaman rayuwa, mutane da yawa da ke zama a wuraren da ke bakin tekun kudancin kasar Sin sun tafi zuwa kasashen waje don tsirar da kansu daga zaman talauci sosai. Babban wansa mai suna Sun Mei shi ma ya kama hanyar nan, sa'anna ya sami nasara wajen zaman rayuwa a kasar Amurka, daga nan sai ya karbi Mr Sun Yat-sen zuwa wajensa don yin zama tare da shi. Daga lokacin da ya cika shekaru 13 da haihuwa, Mr Sun Yat-sen ya sami tarbiyya sosai a kasar Amurka da Hongkong bi da bi, kuma ya amince da tunanin masu jarin hujja na kasashen yamma. Bayan da ya balaga, Mr Sun Yat-sen ya sami horon da aka yi masa wajen aikin likitanci a cikin shekaru da yawa, ya yi fatan kawar da wahalolin da jama'ar kasar Sin suka sha ta hanyar yin amfani da kayayyakin likitanci, amma hakikanan abubuwan da ake yi a zamantakewar al'umma ya karya mafarkinsa kwata kwata.


1 2 3