
Yanzu, a nan birnin Beijing, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar koli ta kasar tana zaman taronta na wannan shekara. A ran 6 ga wata, bi da bi Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar suka halarci tattaunawar da wakilan lardin Hunan a kudancin kasar da na lardin Gansu a yammacin kasar suka yi, inda suka yi shawarwari tare da su a kan manyan al'amuran kasar.

Bayan da Mr Hu Jintao ya saurari jawabi da wakilan 10 na bangarori daban daban suka yi a tsanake, sai ya bayyana ra'ayoyinsa a kan aiwatar da ayyukan gwamnatin kasar musamman don bunkasa aikin noma da na masana'antu. Ya ce, ya kamata, mu daidaita matsaloli da ke jawo jama'a sosai game da moriyarsu da kyau, bisa burinsu na namen samun wadata da daidaici da zaman kwanciyar hankali. Ya kamata, mu kara kokari wajen tallafa wa aikin gona da kauyuka, a yi kokari wajen bunkasa aikin gona na zamani, da sa kaimi ga kara yawan kudin shiga da manoma ke samu, da horar da sabbin manoma. Sa'an nan kuma ya kamata, mu tsaya tsayin daka wajen bin hanyar raya aikin masana'antu na zamani, mu yi kokari wajen raya sana'o'I masu rinjaye, mu kara kwarewa wajen yin kirkirowa cikin cin kashin kai, kuma mu yi kokari wajen tsimin kamashi da kare muhalli.
Firayim minista Wen Jiabao ya yi shawarwari tare da wakilan a kan yadda za a kara kokari wajen daidaita batutuwan aikin gona da kauyuka da manoma da inganta manyan ayyuka da kare yanayin kasa da sauransu. (Halilu)
|