Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 18:27:50    
Akidar jituwar duniya tana dacewa da cigaban zamani, in ji ministan harkokin waje na Sin

cri
Ran 6 ga wata, Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana cewa, shawarwari da Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin da gwamnatin kasar suka gabatar dangane da raya zaman al'umma mai jituwa da duniya mai jituwa suna dacewa da ci gaban zamani da burin jama'a da kuma moriyarsu.

Yayin da yake amsa tambayar da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya yi masa a gun taron manema labaru na gida da waje na taro na biyar na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta goma, Mr Li Zhaoxing ya ce, a fannin diplomasiya, kasar Sin tana kokarin yin zaman tare a tsakanin kasa da kasa cikin lumana, da yin ma'amala cikin daidaici, da yin hadin guiwa don moriyar juna, da neman samun bunkasuwa tare, da zaman jituwa da makwabciya da nuna wa juna amincewa, da neman warware rikici a tsakanin ta hanyar tattaunawa da sauran hanyoyin diplomasiya, da sauransu.

Yayin da wani dan jarida ya yi masa tambaya cewa, kafofin watsa labaru sunna yin suka ga kasar Sin cewa, kasar Sin ba ta son kara matsa lamba ga wasu kasashe da ke taka hakkin dan adam da cin hanci da rashawa bisa sanadiyyar rashin yin shisshigi cikin harkokinsu, sai Mr Li Zhaoxing ya amsa cewa, a cikin tsarin ka'idojin majalisar dinkin duniya an tsai da ka'idar rashin yin shisshigi cikin harkokin gida na wata kasa. Bai kamata wata kasa ta yi shisshigi cikin harkokin gida na wata kasa dabam ba. A hakika dai, nuna wa juna girmamawa da rashin yin shisshigi cikin harkokin gida sharudda ne da suka wajabta, yayin da ake raya zaman al'umma mai jituwa da kuma duniya mai jituwa. (Halilu)